Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar ADC da sauran ƴan Najeriya da su kwantar da hankalinsu bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke kan rikicin shugabancin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce saɓanin rahotannin da ake yaɗawa, hukuncin kotun bai soke zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ADC ta gudanar domin tsayar da ƴan takararta a zaɓen 2027 ba.
Ya zargi wasu da yaɗa bayanan da ba su dace ba, yana mai cewa ikirarin cewa hukuncin kotun ya kawo ƙarshen takarar shugaban ƙasa ta ADC wani yunƙuri ne na raunana ƴan adawa da kuma rikitar da al’umma.
Atiku ya bayyana cewa hukuncin kotun ya taƙaita ne ga zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da kuma wa’adin shugabannin kwamitocin riƙo na jihohi, ba ya da alaƙa da zaɓen fidda gwani ko tsayar da ƴan takara.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar na girmama hukuncin kotun, amma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli domin neman hukunci na ƙarshe kan lamarin.
A ƙarshe, Atiku ya buƙaci magoya bayan ADC da kada su karaya, yana mai jaddada cewa gwagwarmayar ceto Najeriya ba za ta tsaya saboda hukuncin kotu guda ɗaya ba.
