Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahoton cewa ta ware sama da naira miliyan 200 domin gina ajujuwa a wata makaranta da ba ta wanzu a Ƙaramar Hukumar Sumaila.
Cibiyar Tracka mai sa ido kan ayyukan gwamnati ce ta yi ikirarin cewa an ware naira miliyan 235 da dubu 400 domin gina ajujuwa a makarantar GGSSS Massu da ke yankin Massu a Ƙaramar Hukumar Sumaila.
Tracka ta ce binciken da ta gudanar bayan ziyartar yankin a watan Yunin 2026 ya nuna cewa ba ta samu wata makaranta mai suna GGSSS Massu ba, yayin da mazauna yankin suka tabbatar mata da cewa babu irin wannan makaranta a yankin.
Sai dai mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya musanta zargin, yana mai cewa gwamnatin jihar ba ta taɓa ware kuɗin da aka ambata domin gudanar da irin wannan aiki ba.
Sanusi Bature ya yi kira ga cibiyoyin sa ido kan ayyukan gwamnati da su ƙara fahimtar dokokin kasafin kuɗi kafin su gabatar da koke-koke ko zarge-zarge.
A nata bangaren, Tracka ta ce rahoton Kasafin Kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya nuna cewa an ware kuɗin ne domin gina bene mai ɗauke da ajujuwa takwas, ofis da ɗakin ajiya a makarantar GGSSS Massu.
