Rahotanni daga Daily Nigerian sun ce ana zargin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL, da ɗaukar sabbin manyan ma’aikata da masu matsakaicin matsayi ba tare da bayyana guraben aikin ga jama’a ba, lamarin da wasu ke cewa ya saɓa da ƙa’idar Federal Character.
Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa an gudanar da ɗaukar ma’aikatan ne a lokaci guda da shirin bai wa wasu ma’aikata damar yin ritaya da son rai, ba tare da talla ko bayyana ƙa’idojin zaɓen waɗanda aka ɗauka ba.
Haka kuma, masu ruwa da tsaki sun soki Dokar Zartarwa ta 9 (Executive Order 9) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya, wadda ta karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin binciken mai a sabbin yankuna zuwa Asusun Tarayya.
Rahoton ya ce wannan mataki ya dakatar da amfani da Frontier Exploration Fund, asusun da Dokar Masana’antar Mai ta ƙasa ta kafa domin tallafa wa binciken mai a yankunan Chad Basin, Sokoto Basin, Bida Basin, Benue Trough da Gongola Basin, waɗanda ake kallon su a matsayin wuraren da ke da damar samar da sababbin rijiyoyin mai.
Masana sun yi gargadin cewa dakatar da wannan asusu na iya kawo cikas ga shirin ƙara yawan albarkatun man Najeriya da kuma faɗaɗa aikin haƙo mai zuwa yankunan da ba a bunƙasa ba.
A ɓangaren zargin ɗaukar ma’aikata kuwa, rahoton ya ce wasu takardu sun nuna cewa an naɗa sabbin manyan jami’ai guda 15, inda mafi yawansu suka fito daga jihohin Kudancin Najeriya.
Wata majiya a cikin kamfanin ta bayyana damuwa cewa NNPCL ya saba da tsarin buɗaɗɗen ɗaukar aiki, amma abin da ke faruwa yanzu na iya haifar da asarar ƙwararrun ma’aikata da gogewar da aka tara tsawon shekaru.
Masu ruwa da tsaki sun kuma bayyana cewa dakatar da tallafin binciken mai a Arewacin Najeriya na iya rage damar gano sabbin rijiyoyin mai, da kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a yankunan da abin ya shafa.
Sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake nazarin Executive Order 9, tare da tattaunawa da masana kafin aiwatar da manufofin da za su iya yin tasiri ga makomar harkar mai da tattalin arzikin ƙasar.
Sai dai, lokacin da aka nemi jin ta bakin Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPCL, Andrew Odeh, bai mayar da martani ba har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton.
