
Aminu Abdullahi Ibrahim
Babban Daraktan hukumar samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA), Abba Aliyu, ya ce kusan ‘yan Najeriya miliyan 85 har yanzu ba sa samun ingantacciyar wutar lantarki daga babban layin wutar na ƙasa (national grid), lamarin da ke ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’umma.
Aliyu ya bayyana cewa duk da biliyoyin dalolin da aka zuba a ɓangaren makamashi har yanzu akwai babban gibi wajen samar da wutar lantarki ga miliyoyin ‘yan ƙasa.
Ya ce hakan ya sa hukumar mayar da hankali kan faɗaɗa ayyukan samar da wutar da tsarin hasken rana domin kai wuta yankunan da ba su da isassun turaku.
A cewarsa, hukumar na gudanar da ayyukan gina guraren samar da wuta na Solar guda 48 a jihohi 19 na ƙasar nan domin ƙara yawan al’ummomin da za su samu ingantacciyar wutar lantarki ba tare da dogaro da babban layin turo wuta ba.
Ya kuma jaddada cewa bunƙasa samar da wutar lantarki ba wai zai inganta rayuwar jama’a kaɗai ba, har ma zai ƙarfafa masana’antu, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
