Gwamnatin Kano ta ce zata yi nazari kan bukatar da ƙungiyar tsaffin kansiloli masu gafaka ta gabatar mata na duba yiwuwar ba su tallafin kuɗi da filaye kamar yadda aka yiwa tsofaffin zaɓaɓɓun kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi a baya, domin rage musu raɗaɗin rayuwa.
Kwamishinan yaɗa labarai da Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan lokacin da ƙungiyar tsofaffin Kansilolin masu gafaka na ƙananan hukumomi 44 suka kai masa ziyara.
A cewar waiya tallafin da Gwamnan ya baiwa waɗanda suka amfana a baya, ba wani hakki ne na doka ba, illa halin karamci da taimakon al’umma da Gwamnan ke da shi, tare da yin alƙawarin isar da buƙatar ƙungiyar ga Gwamna Abba.
Da yake jawabi tunda farko, Jagoran tawagar, Malam Ahmad Danlabaran, ya ce an kafa ƙungiyar ne domin haɗa kan tsofaffin Kansilolin masu gafaka da bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki, siyasa da zamantakewar al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Waiya na sukar masu hamayya da tallafawa tsofaffin Kansilolin da Gwamna Abba yayi a baya, yana mai cewa gwamnati mai kishin jama’a ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen taimakawa kowa idan hali ya ba ta dama.
