Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya raba kyautar filaye 1,540 da naira miliyan100 ga shugabannin ƙungiyar masu goyon bayan APC a matakin rumfunan zaɓe wato ‘yan akwati, da nufin ƙarfafa musu gwiwar tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027 mai tunkarowa.
Gwamnan ya bayyana bada kyautar ne lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ƙungiyar ta ‘ yan akwati waɗanda zasu yiwa jam’iyyar APC aiki a matakin mazaɓu a lokacin zaɓe.
Gwamnan ya ce yunƙurin ƙarfafa jam’iyya tun daga tushe zai taimaka wajen tabbatar da samun nasarar Shugaba Bola Tinubu da kuma sauran ‘yan takarar APC a dukkan zaɓukan da za’a gudanar
A cewar gwamna Abba, sake zaɓen Shugaba Tinubu zai bada damar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa, wanda hakan ce ta sanya gwamnati baiwa ƙungiyar kyuatar filaye da tallafin naira miliyan ɗari domin gudanar da ayyukanta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa tunda farko a jawabin sa, mai baiwa gwamna Abba shawara kan harkokin siyasa, Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya ce tallafin shi ne matakin farko na shirin tattara magoya bayan APC gabanin zaɓen 2027, inda ya ce ‘yan Akwatin kaɗai na da ƙarfin tarawa shugaba Tinubu ƙuri’u sama da miliyan ɗaya.
