Gwamnatin Kano ta dakatar da shirin bayar da magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro na lokacin damina a faɗin jihar, domin baiwa kwamitin ƙwararru damar gudanar da cikakken bincike kan yadda ake tsarawa da aiwatar da shirin.
Kwamshinan lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce Matakin ya biyo bayan kafa wani babban kwamitin bincike da Ma’aikatar ta yi, wanda aka ɗorawa alhakin nazarin yadda aka tsara shirin, rabon magunguna, gudanar da ayyuka da duba duk bayanan da suka shafi aiwatar da shirin.
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, jami’in yada labaran ma’aikatar Nabulisi Abubakar K/Na’isa ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take, inda kuma aka tsayar da dukkan ayyukan da ake gudanarwa na rabon magunguna da wayar da kan al’umma har sai an kammala binciken.
Nabulisi ya ce Kwamitin binciken dai yana ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar yaƙi da cutar ƙanjamau ta Kano, Dr Usman Bashir, kuma ya haɗa da shugabannin manyan hukumomin lafiya na jihar domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da bincike.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Nabulisi na cewa tuni aka dakatar da Manajan Shirin daga aiki, tare da miƙa ragamar gudanar da shirin na wucin gadi ga babban jami’in da ya fi kowa matsayi a cikin shirin.
