Gwamnatin Kano ta ce ta ware naira miliyan dari uku domin tallafawa amaren da za su amfana da shirin ta na auren gata da Hukumar Hisbah za ta gudanar a juma’ar nan mai zuwa, domin yin jari sana’o’in da zasu dogara da kan su da taimakawa iyalan su a rayuwar aure.
Shugaban hukumar Hisba ta Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bita ga angwaye da amaren da za’a aurar mai taken gudunmawar auren gata wajan samar da zamantakewa ta gari.
Sheikh Daurawa yace kowace amarya za ta karɓi naira dubu dari biyu a matsayin jari da sadaki, inda ya ce za’a tura kuɗin ne kai tsaye zuwa asusun bankin da aka budewa kowace amarya, baya ga cikakkun kayan ɗaki da cewa gwamnatin Kano ta samar musu.
Sheikh Daurawa ya ce akwai angwaye kusan 200 da aka dakatar daga shiga shirin auren, saboda samun su da matsalolin dake da alaka da lafiya, yayin da aka cire wasu daga cikin amaren kuma saboda samun su ɗauke da juna biyu, tare da tabbatar da cewa wadanda aka samu da rashin lafiyar da zarar sun warke hukumar zata kira su domin daura nasu auren.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sheikh Daurawa na yin kira ga angwayen da su riƙi matansu da amana, su guji cin mutuncin su, tare da shawartar amaren da su yi haƙuri da mazajensu da yi musu biyayya, yana mai cewa Hukumar Hisbah ba ta amince da rabuwa a auren ba har sai anje gabanta ta bi matakan da shari’a ta amince da su.
