Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen aiwatar da cikakken shirin bunƙasa jihar domin hanzarta ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC a rumfunan zaɓe wadanda aka fi sani da ‘yan akwati na ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da ingantaccen shugabanci da kyautata rayuwar al’umma.
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ba za ta bari siyasa ko wasu matsin lamba su karkatar da ita daga aiwatar da ayyukan raya ƙasa ba, yana mai cewa za’a ci gaba da gudanar da ayyukan da za su bunƙasa tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa da kuma ayyukan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa irin nasarorin da gwamnatinsa ke samu za su ƙara tabbatar da goyon bayan al’ummar Kano gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na buƙatar shugabannin da su kasance masu haɗin kai tare da ƙara himma wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya ga jam’iyyar a rumfunan zaɓe, unguwanni da ƙananan hukumominsu.
