Gwamnatin Kano ta ce al’ummar ƙaramar hukumar Warawa sun fara samun ruwan famfo a karon farko cikin fiye da shekaru biyar, bayan da gwamnatin jihar ta fara gwajin tura ruwa ta layin rarraba ruwa na yankin.
Kwamshinan Ma’aikatar Albarkatun ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi Dr Dahiru M Hashim ne ya bayyana hakan ya biyo bayan duba ayyukan da ake gudanarwa a matatun ruwan Wudil da Joda, inda aka tabbatar da cewa matatar Wudil za ta rika samar da ruwa akai-akai ga al’ummar Wudil bayan inganta wutar lantarkin da take samu zuwa tsakanin sa’o’i 18 zuwa 22 a kullum.
Dr Dahiru ya ce an kuma fara gwajin tura ruwa ta layin Warawa domin gano wuraren da bututun ke zubar da ruwa da kuma tabbatar da ƙarfin isar ruwa wajen da aka tura shi, inda ya ce ana kuma sa ran ruwan zai rika isa har zuwa Rijiyar Gwan-gwan, yayin da za’a fara aikin gwaji a layukan Gaya da Dawakin Kudu nan ba da jimawa ba.
Hakazalika, Dr Hashim ya ce matatar ruwan Joda ta koma samar da ruwa ga wasu al’ummomi a ƙaramar hukumar Gabasawa, inda rijiyoyi bakwai ke aiki a yanzu, tare da shirin ƙara wasu biyar domin matatar ta kai cikakken ƙarfin aikinta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa jami’an kula da aikin sun ce ana ci gaba da gyaran gine-gine da katanga a matatun ruwan domin tabbatar da ingantaccen aiki da kuma kare kayayyakin gwamnati, tare da yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan goyon bayan da yake bai wa ɓangaren samar da ruwan sha a jihar.
