Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa ya bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Kula da Hakar Man Fetur ta NUPRC da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da wasu hukumomin gwamnati wa’adin sa’o’i 72 su bayyana a gabansa domin amsa tambayoyi kan rahotannin binciken kuɗaɗen man fetur.
Kwamitin ya ɗauki wannan mataki ne bayan hukumomin sun gaza halartar zaman sauraron jama’a da aka shirya domin nazarin rahotannin NEITI na shekarun 2021, 2022 da 2023, lamarin da ya hana zaman ci gaba kamar yadda aka tsara.
Shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo, ya ce an aika gayyata ga hukumomin tun da wuri, amma ba su halarta ba kuma ba su bayar da wani uzuri a hukumance ba.
Ya gargade su da cewa idan ba su bayyana cikin wa’adin da aka ba su ba, Majalisar za ta iya ɗaukar matakan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Kwamitin ya ce binciken na da nufin tantance yadda aka gudanar da kuɗaɗen shiga, da wadanda aka turawa gwamnati da sauran bayanan kuɗi a ɓangaren mai da iskar gas, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen sarrafa albarkatun ƙasar nan.
