Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa, EFCC, ta fara bincike kan zargin watsi da aikin gyaran wani ɓangare na hanyar Asaba-Onitsha a jihar Delta, bayan rahotannin cewa an biya ɗan kwangilar kusan naira biliyan 14
Wani babban jami’in EFCC ya tabbatar da cewa masu binciken hukumar sun ziyarci wurin aikin domin tabbatar da halin da aikin yake ciki, yana mai cewa binciken yana matakin farko
Binciken ya biyo bayan ƙorafin wani mai fafutuka kuma mawallafin The Common Good Letter, Reverend David Ugolor, wanda ya bukaci EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki yadda aka bayar da kwangilar, yadda aka samar da kuɗaɗen aikin da kuma yadda aka gudanar da shi
A watan Agustan 2026, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya nuna damuwa kan aikin, yana zargin kamfanin Hartland Nigeria Limited da kasa kammala aikin mai tsawon kusan kilomita 11 duk da cewa an biya shi kusan naira biliyan 14
Rahotanni sun ce an kiyasta cewa kusan kashi 40 cikin 100 ne kawai na aikin aka kammala. Ministan ya kuma buƙaci a binciki takardun shaidar da aka bayar dangane da aikin da kuma yiwuwar dawo da kuɗaɗen gwamnati idan bincike ya tabbatar da laifi
