Hukumar Plateau Express Services Group, wadda ke kula da motoci ce, ta sanar da cewa dokar babu takunkumin fuska, babu shiga mota za ta fara aiki daga Talata, 8 ga Satumba, kuma za ta ci gaba har sai an bada wani sabon umarni.
Hukumar ta ce an tanadi wasu takunkuman fuska a wuraren hawa motocin, amma ta shawarci fasinjoji su riƙa zuwa da nasu, saboda waɗanda aka tanada ba za su isa ga kowa ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da jihar ke ƙara ɗaukar matakan dakile barkewar cutar ta mashako.
