Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man fetur ta Dangote za ta zama matatar da ta fi kowacce girma a duniya nan da shekarar 2028.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin bikin rattaba hannu kan shirin sayar da hannayen jarin matatar ga jama’a, wato IPO.
Ya ce matatar mai karfin tace ganga 700,000 a kowace rana, ita ce mafi girma a Afirka, sannan kuma ita ce matata mai layin tace mai guda daya mafi girma a duniya.
“Yau rana ce mai muhimmanci ba ga kamfanin mu ba kawai, har ma ga ’yan Najeriya da Afirka baki daya,” in ji Dangote.
Ya ce aikin gina matatar ya fara ne sama da shekaru 10 da suka gabata, inda bankuna suka taimaka wajen samar da kudaden aikin, duk da cewa a lokacin ba su ma ga wurin da za a gina matatar ba, kuma ba a samu lasisin aikin ba.
Dangote ya ce hakan ya nuna cewa babu abin da ba zai yiwu ba idan aka samu jajircewa da mayar da hankali.
“Mun koyi darasi ta hanya mai wahala, kuma ba za mu iya mayar da Afirka masana’antu ba idan ba mu tabbatar da samar da makamashi ba,” in ji shi.
Ya ce saboda haka kamfanin ya kara mayar da hankali kan samar da wadataccen makamashi a Najeriya, tare da fadada ayyukansa na masana’antu a sauran kasashen Afirka, ciki har da Habasha, Kenya, Tanzania da Namibia.
Dangane da shirin sayar da hannayen jarin matatar ga jama’a, Dangote ya ce kowa zai samu damar mallakar hannun jari, ba tare da ware matsala ba.
“Babu wanda aka ware wajen mallakar hannayen jarin. Muna son duk wani mutum da ke zaune a nahiyar Afirka ya kasance cikin wannan tafiya,” in ji shi.
A nasa bangaren, babban jami’in gudanarwa na matatar Dangote, David Bird, ya ce matatar na samar da man fetur ga Najeriya, yayin da take kuma mayar da hankali kan kasuwannin kasashen Yammacin Afirka.
Bird ya ce kayayyakin da matatar ke samarwa sun riga sun isa kasuwannin duniya, musamman man jiragen sama, inda ya ce matatar ta zama daya daga cikin manyan masu samar da man jiragen sama ga Turai.
“Babu lokacin da ya fi yanzu dacewa da mu nuna wa duniya ingancin kayayyakinmu na matakin duniya, domin mu ne babban mai samar da man jiragen sama ga Turai,” in ji Bird.
Ya ce matatar ta samu gagarumar nasara cikin watanni shida da suka gabata, inda ayyukanta suka taimaka wajen rage tasirin matsalolin samar da man fetur da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya da Ukraine suka haifar.
Bird ya kara da cewa matatar na iya tace nau’o’in danyen mai daban-daban tare da samar da kayayyaki ga kasuwannin duniya.
Ya ce an riga an kammala shirye-shiryen fasaha da sayen kayayyakin da ake bukata domin fadada matatar, yayin da babban aikin da ya rage shi ne gina sassan fadadar.
