A cikin wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Hanga ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.
Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari da tunani mai zurfi, yana mai cewa ya bar jam’iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu al’amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.
Hanga ya miƙa godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar a matakin mazaɓa, kwamitin gudanarwa da daukacin mambobin NDC bisa irin goyon baya, dama da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, Sanata Rufai Hanga bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba ko kuma matakin siyasar da zai ɗauka bayan ficewarsa daga NDC.
