Mataimakin shugaban kasa, sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ’yan Najeriya da su kasance masu haƙuri da kuma nuna fahimta ga shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar ya ɗauki matakai masu wahala domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durƙushewa.
Shettima ya bayyana cewa wasu daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, duk da cewa sun jawo wa al’umma matsin rayuwa, sun kasance wajibi ne domin kauce wa mummunan yanayin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su yi wa shugaban ƙasar uzuri bisa irin waɗannan matakai, tare da fahimtar cewa gyaran tattalin arziki na buƙatar jajircewa da kuma ɗaukar matakan da ba lallai ne su yi wa kowa daɗi ba.
Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin samar da ingantacciyar makoma ga ƙasar, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.
Sai dai kalaman Shettima na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi, hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsin tattalin arziki da ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum.
