The Economist ta yi hasashen cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na iya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa da za’a gudanar a shekarar 2027, duk da matsin tattalin arziki, matsalolin tsaro da kuma rashin gamsuwar wasu ’yan Najeriya da salon mulkinsa.
A wani rahoto da mujallar ta wallafa a ranar 1 ga Oktoba, ta bayyana cewa akwai wasu dalilai da za su iya taimaka wa Tinubu wajen samun nasara, ciki har da kasancewarsa shugaban ƙasa mai ci, ƙarfin tsarin jam’iyyar APC, rarrabuwar kawunan ’yan adawa da kuma yadda addini da ƙarancin fitowar masu zaɓe za su iya tasiri ga sakamakon zaɓen.
Mujallar ta kuma yi nuni da cewa, duk da cewa wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun samu yabo daga masu zuba jari, har yanzu ba su haifar da sauƙin rayuwa ga mafi yawan ’yan Najeriya ba, ta kuma bayyana cewa matsalolin tsaro da tsadar rayuwa na iya rage farin jinin shugaban ƙasar.
Sai dai kwamitin yakin zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya yi watsi da hasashen, yana mai cewa hasashe ba hukunci ba ne.
Daraktan yaɗa labarai da sadarwa na yakin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya ce abubuwan da mujallar ta lissafa ba sa nufin cewa ’yan Najeriya sun amince da ci gaba da mulkin Tinubu ba, ya jaddada cewa halin tattalin arzikin ƙasa, musamman yadda kuɗin shiga ke kasa wa mutane biyan buƙatunsu na yau da kullum, shi ne zai fi tasiri ga zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.
Shaibu ya kuma ƙalubalanci ra’ayin cewa ƙarancin fitowar masu zaɓe na iya taimaka wa shugaban ƙasa mai ci, yana mai cewa rashin fitowar jama’a a zaɓen 2023 na iya kasancewa sakamakon rashin sha’awa, matsalar tsaro, rashin amincewa da tsarin zaɓe ko kuma matsalolin gudanar da zaɓe.
Ya ce ADC na da yakinin cewa ’yan Najeriya za su yi amfani da ƙuri’unsu wajen bayyana matsayarsu a zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa hasashen wata jarida ba zai iya maye gurbin ikon jama’a na zaɓen shugabanninsu ba.
