Gwamnatin Kano ta bukaci ‘yan kasuwa da masu zuba hannun jari su karkata hankalinsu zuwa fannin tsaftar muhalli domin inganta lafiyar al’umma, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi, Dr Dahiru M Hashim, ne ya bayyana hakan yayin taron ƙaddamar da shirin haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu kan tsaftar muhalli da aka gudanar a Kano.
Dr Dahiru ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ɗaukar fannin tsaftar muhalli a matsayin muhimmin ginshiƙin kare lafiyar jama’a da zama wata babbar dama ta zuba jari ga ‘yan kasuwa.
Kwamshinan ya ce ƙaruwar yawan al’umma da Kano ke samu a kullum yana buɗe ƙofofi ga masu zuba jari a fannoni kamar gina bandakunan jama’a, sarrafa bayan gari da kuma sake amfani da shara wajen samar da wasu albarkatun.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na bayyana wasu daga matakan da gwamnatin Kano ke ɗauka, ciki har da aiwatar da dokar kare muhalli, farfaɗo da hukumomin kula da muhalli, gyaran cibiyoyin tace ruwa da kuma ƙaddamar da shirin Smart Kano Waste and Sanitation Initiative, wanda zai inganta ayyukan tsaftar muhalli ta hanyar amfani da fasahar zamani da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.
