Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya ziyarci Tinubu a Legas, bayan dawowarsa daga birnin New York na ƙasar Amurka, inda ya wakilci shugaban ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai a kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ne ya bayyana ziyarar a wani saƙo da ya wallafa a ranar Asabar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar, Shettima ya ce ya ci gaba da tattaunawa da Tinubu a kai a kai a lokacin da shugaban ƙasar yake rangadin aiki a ƙasashen waje, inda suke musayar bayanai kan muhimman al’amuran ƙasa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma kare wasu matakan tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗaɗen waje, yana mai cewa matakan sun taimaka wajen ceto tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa.
Sai dai Shettima ya bayyana cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, amma ya buƙaci su yi haƙuri, yana mai cewa gwamnati na shirin bullo da shirye-shirye domin rage wa al’umma raɗaɗin tsadar rayuwa.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin ƙaddamar da wasu shirye-shiryen tallafi, ciki har da samar da babura masu ƙafa uku masu amfani da wutar lantarki, motocin bas da motocin haya a yankin Arewa maso Gabas, tare da wasu shirye-shirye na tallafa wa ɗalibai da sauran masu ƙaramin ƙarfi.
Ziyarar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan dawowar Shettima daga taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya gabatar da jawabin Najeriya tare da bayyana matsayar ƙasar kan sauye-sauyen da ake buƙata a majalisar tsaro ta majalisar ɗinkin Duniya, da kuma ƙarin wakilcin Afirka a matakin duniya.
