Bayan kammala yajin aikin gargadi na kwanaki uku, ma’aikatan gwamnati sun bai wa gwamnatin tarayya sabon wa’adi domin ta dauki matakan da suka dace kan bukatunsu.
Ma’aikatan sun bayyana cewa matakin nasu ya biyo bayan rashin samun gamsasshen bayani ko warware wasu daga cikin matsalolin da suka dade suna gabatarwa ga gwamnati.
Sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa wajen duba bukatunsu tare da daukar matakan da za su kawo karshen matsalolin da ke tsakaninsu.
Jaridar vanguard ta rawaito cewa ma’aikatan na bayyana cewa idan gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace cikin wa’adin da suka sanya ba, za su iya daukar wasu matakai na gaba domin matsa mata ta saurari bukatunsu.
