
Rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP ya ɗauki sabon salo bayan ɓangarorin Wike da Tanimu Turaki, sun gabatar da shahadar takara ga mabanbantan yan takararsu.
Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan kafin Hukumar Zaɓe INEC, ta fara bai wa jam’iyyun siyasa lambobin shiga tsarin da ake amfani da shi wajen tura sunayen ‘yan takara.
Kowanne ɓangare ya bayyana kansa a matsayin halastaccen shugabancin PDP, tare da nuna kwarin gwiwar cewa INEC za ta amince da sunayen ‘yan takarar da ya gabatar.
A taron ɓangaren da Wike ke marawa baya, shugabannin jam’iyyar sun miƙa takardun shaidar nasara ga Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, tare da sauran ‘yan takarar gwamnoni da na majalisun dokoki, ciki har da Isa Ali Pantami na jihar Gombe.
A gefe guda kuma, Turaki ya ce ɓangarensa ya tantance ‘yan takara kafin ba su takardun shaidar nasara, inda ya tsayar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Wannan dai na ƙara nuna yadda rikicin shugabanci ke ci gaba da raba kan PDP, yayin da jam’iyyar ke shirin shiga babban zaɓen shekarar 2027.
Ana sa ran matakin da INEC za ta ɗauka wajen karɓar sunayen ‘yan takara zai kasance muhimmin abin da zai ƙara bayyana inda rikicin ya dosa.
