- Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Opada-Olowa a ƙaramar hukumar Dekina ta Jihar Kogi, inda suka yi garkuwa da shugaban makarantar, jami’in kula da jarabawar NECO da kuma ɗalibai huɗu.
Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, yayin da ake rubuta jarabawar NECO.
Shaidu sun ce maharan sun shiga garin suna harbe-harbe domin tarwatsa jama’a kafin su kutsa cikin makarantar.
Wani shugaban al’umma, Sunday Alkali, ya ce maharan sun fara ja da baya, bayan sun ga mutane da yawa amma daga bisani suka dawo suna harbe-harbe lamarin da ya sa kowa ya tsere domin tsira.
Bayan harbin ya lafa, mazauna yankin sun ce sun tarar da takardun jarabawa a warwatse a ajujuwa, yayin da ba a ga ɗalibai ko ma’aikatan makarantar ba.
Daga baya an tabbatar da cewa waɗanda aka sace sun haɗa da shugaban makarantar Malam Nyada Daniel, jami’in kula da jarabawar NECO Malam Solomon Audu, da kuma ɗalibai huɗu.
Mazauna yankin sun ce adadin ɗaliban da aka sace bai yi yawa ba saboda a lokacin ana rubuta jarabawar Literature in English, wadda ba ta da yawan masu rubutawa kamar Turanci ko Lissafi.
