Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya baiwa ƙungiyar mahautan jihar tallafin naira miliyan 100, tare da yin alƙawarin gina musu kasuwa ta zamani domin inganta harkokin yanka nama, tabbatar da tsafta da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rabon tallafin kayan aiki ga mahauta 1,900 a faɗin jihar, inda ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ƙarfafa sana’o’in da ke samar da ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga ga al’umma.
Gwamnan ya ce gina kasuwar zamani zai samarwa mahautan ingantaccen muhalli da gudanar da sana’arsu cikin tsafta da tsari, tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci da kare lafiyar masu saye da masu sayarwa.
Wasu daga cikin mahautan da suka amfana da tallafin kayan aikin, sun yabawa Gwamna Abba bisa tallafin, inda suka ce zai taimaka musu wajen bunƙasa sana’ar fawa da inganta rayuwar su tare da alƙawarin ci gaba da baiwa gwamnati cikakken haɗin kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamna Abba ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin, su yi amfani da shi yadda ya dace domin faɗaɗa sana’o’insu, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa da masu sana’o’i domin rage talauci da haɓaka tattalin arzikin Kano.
