Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa ba za ta amince da hukuncin kotun da ya takaita ayyukanta a wasu titunan Jihar Kano ba, inda ta tabbatar da cewa za ta ɗaukaka ƙara domin kalubalantar hukuncin.
Kakakin hukumar a Jihar Kano, Abdullahi Labaran, ya ce FRSC ba ta gamsu da hukuncin kotun ba, saboda haka za ta nemi babbar kotu ta sake duba shari’ar.
Ya bayyana cewa kusan kashi 90 cikin 100 na titunan da ke Jihar Kano mallakin Gwamnatin Tarayya ne, yana mai jaddada cewa ayyukan hukumar a jihar ana gudanar da su ne a kan irin waɗannan tituna.
Wannan na zuwa ne bayan wata kotu ta yanke hukunci a ƙarar da lauya Abba Hikima ya shigar, inda ta hana FRSC gudanar da ayyukanta a titunan da ba mallakin Gwamnatin Tarayya ba.
