Hukumar Kwastam ta Najeriya, Shiyyar Kano da Jigawa, ta kama tankokin man jirgin sama guda biyu da aka shigo da su ƙasar ba tare da bin ƙa’idar doka ba.
Kodinetan Sashen Kula da Man Jirgin Sama da Dangoginsa na Hukumar Kwastam, Mataimakin Kwanturola Abubakar Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake miƙa tankokin da aka kama ga Hukumar Kula da Safarar Man Jirgin Sama ta Ƙasa.
Da yake karɓar kayan, Injiniya Nazifi Lawan Bashir, jami’i a Hukumar Kula da Sarrafawa da Rarraba Man Jirgin Sama, ya ce hukumarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da safarar haramtattun kayayyaki da tabbatar da bin dokokin kasuwanci domin kare tattalin arzikin ƙasa da kuma inganta tsaron al’umma.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen dakile ayyukan masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba.
Wakilinmu, Umar Ahmad El-Kanawy, ya ruwaito cewa Hukumar Kwastam ta kuma yi kira ga masu shigo da kayayyaki da su riƙa bin hanyoyin da doka ta tanada wajen gudanar da kasuwancinsu, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin karya dokokin hukumar zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
