Hukumar leken asiri kan harkokin kuɗi ta Najeriya, NFIU, ta ce ta gano wata sabuwar hanyar rarraba kuɗaɗen da ake amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci, ciki har da amfani da asusun bankunan mata da kuma lambobin wayar da aka yi wa rajista da sunayen mutanen da suka mutu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa NFIU ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na shekara ta 2025, inda ta ce wasu masu taimaka wa ’yan ta’adda daga ƙasashen waje na amfani da kafafen sada zumunta wajen neman gudummawa da sunan tallafa wa ayyukan jin ƙai ko ilimi.
A cewar rahoton, ana neman mutane da dama su bayar da kuɗaɗen da yawansu ke tsakanin dala 50 zuwa 500, domin kauce wa tsarin gano manyan mu’amalolin kuɗi da ake amfani da su wajen yaƙi da safarar kuɗaɗen haram.
NFIU ta ce daga bisani ana tattara kuɗaɗen a wani babban asusu, sannan a rarraba su tare da turo su Najeriya ta hanyar kamfanonin aika kuɗi da manhajojin tura kuɗaɗe.
Ta ce wasu daga cikin mutanen da ake amfani da su wajen karɓar kuɗaɗen sun haɗa da ɗalibai, masu ƙananan sana’o’i da kuma ’yan uwa da abokan arziki.
Hukumar ta kuma ce ana amfani da asusun bankunan mata a matsayin wakilci, inda wasu maza da ke da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci ke sarrafa katunan ATM, lambobin sirri da kuma manhajojin banki na asusun.
Bugu da ƙari, rahoton ya ce wasu masu taimaka wa ’yan ta’adda na amfani da lambobin waya da ba su da alaƙa da ainihin masu asusun, ciki har da lambobin da aka yi wa rajista da sunayen mutanen da suka rasu.
NFIU ta ce hakan na taimaka musu wajen ɓoye alaƙar da ke tsakanin asusun banki, layin waya da lambar BVN, lamarin da ke ƙara wahalar gano ainihin waɗanda ke gudanar da hada-hadar kuɗin.
Hukumar ta kuma gano cewa wasu ƙungiyoyin ta’addanci na amfani da kalmomi na musamman, (code), lambobi da bayanan sirri a wajen rubuta bayanin hada-hadar kuɗi, domin ɓoye ainihin manufar tura kuɗin.
Rahoton NFIU ya kuma ce zambar kuɗi, damfarar intanet, Ponzi schemes, damfarar da ake yi ta hanyar tara gudummawa da kuma laifukan da suka shafi cryptocurrency na cigaba da zama manyan barazana ga tsarin kuɗin Najeriya.
