Daruruwan shaguna ne suka kone sakamakon wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin a shahararriyar kasuwar Oranyan da ke Ibadan a jihar Oyo.
Wakilin Premier Radio a Ibadan Gaddafi Ahmed da ya ziyarci wurin da abin ya faru, yace gobarar ta fara ne da tsakar daren Lahadi, inda ta shafi sassa daban-daban na kasuwar.
Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai yan arewa da ke ciniki a kasuwar da kuma wadanda kan kai kaya.
Wani bahaushe da ya shafe shekaru sama da 30 yana ciniki a kasuwar ya shaida wa Wakilinmu cewa babu abinda ya tsira dashi, bayan shaginsa baki daya ya ƙone kurmus
“muna kallo kayanmu suna konewa, tunda tufafi ne kaga yana da cin wuta kuma motocin fire service da suka zo Sunyi kaɗan, wutar tafi karfin su”
Har yanzu ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ko kuma yawan asarar da aka tafka ba.
