Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Kano ta kama wani matashi Abubakar Muhammad wanda aka taba yin garkuwa da shi, da zargin aikata laifin safarar makamakai a karamar hukumar Gezawa.
Rahotanni sun ce an kama wanda ake zargin ne dauke da bindigogi kirar AK-47 guda 3 da kwanson harsasai guda 2 da Bom din makamin roka guda 4, bayan wani samame da jami’an tsaron suka gudanar bisa bayanan sirri.
Binciken farko ya nuna cewa Abubakar Muhammad dan asalin karamar hukumar Mokwa ne da ke jihar Neja, inda aka kama shi da zargin safarar makaman akan hanyarsa ta kai su karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina lokacin da jami’an DSS suka tare shi a Gezawa.
Da yake yiwa manema labarai karin bayani bayan kama shi, wanda ake zargin ya ce ya karbi makaman ne daga wani mutum Mai Suna Bello a garin Maigatari da ke jihar Jigawa, inda aka umurce shi da ya kai su ga wani mutum a Funtua.
Wanda ake zargin ya ce wadanda suka bas hi dakon makaman sun yi masa alkwarin biyan sa naira dubu 450 da Zarar ya isar da kayan ga wanda zai karba a garin na Funtua.
Jami’an DSS din sun ce suna ci gaba da bincike domin gano wadanda suka samar da makaman da kuma wadanda za’a kaiwa, tare da tantance ko akwai wata kungiyar masu safarar makamai da ke da hannu a lamarin.
Har ila yau, ana binciken hanyoyin da ake amfani da su wajen jigilar makaman domin dakile duk wata hanyar safarar makamai a yankin Arewacin Najeriya.
