Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya lashe babbar lambar yabo ta ƙasa da ƙasa kan jagoranci da bunƙasa ilimi ta duniya, wato International Literacy and Learning Leadership Award, saboda irin gudunmawar da gwamnatinsa ke bayarwa wajen inganta ilimi a jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Lambar yabon wadda ƙungiyar Universal Learning Solutions ta bayar a birnin London, Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2 ne ya karɓi kyautar a madadin Gwamnan, a wani taro da ya haɗa ƙwararru a fannin ilimi, daga sassa daban-daban na duniya.
Masu shirya bikin sun bayyana cewa an karrama gwamnan ne saboda irin manyan matakan da ya ɗauka wajen bunƙasa ilimi, musamman ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar domin ilimi, wanda ke daga cikin mafi girma a Najeriya, da kuma zuba jari wajen inganta koyarwa, faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi da kuma tabbatar da cewa kowane yaro a Kano ya samu damar karatu.
A jawabinsa bayan karɓar kyautar, Sarkin Kanon ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin sauya rayuwar al’umma, tare da yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa baiwa fannin ilimi muhimmanci a manufofin gwamnatinsa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, shi ma a nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar Universal Learning Solutions, Gary Foxcroft, ya ce jajircewar gwamnan wajen saka hannun jari a ilimi, ya nuna irin nasarar da ake samu idan shugabanci ya baiwa bunƙasa ilimin jama’a fifiko.
