Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya baiwa matasa dubu1da suka fito daga ƙungiyoyi daban-daban na ƙananan hukumomi 44 a jihar kyautar fulotai domin tallafa musu da samar da damarmakin zuba jari da dogaro da kai.
Gwamnan, wandaa Sakataren gwamnatin kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya wakilta, ya ce hakan mallakar filayen ga wakilan ƙungiyoyin, wata dama ce ta ɗora rayuwar su akan hanya me kyau.
Gwamna Abba ya ce gwamnati ta tsara wuraren da ta baiwa matasan tare da tanadin makarantu, masallatai, wuraren tsaro da hanyoyi, domin samar da ingantattun al’ummomi masu ci gaba mai ɗorewa.
A nasa jawabin kwamishinan ƙasa na Kano Abduljabbar Umar Garko, ya ce rabon filayen wani ɓangare ne na sauye-sauyen da gwamnati ke yi domin inganta harkokin filaye, yana mai kira ga jama’a da su tabbatar da sahihancin takardun fili kafin yin wata mu’amala.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Garko na yim gargaɗar masu kwacen filaye, damfara, sake sayar da filaye ba bisa ka’ida ba da kuma masu yin gine-gine ba tare da izini ba, da cewa gwamnati za ta ci gaba da inganta tsarin hukumar KANGIS domin sanya mallakar fili ta zama mai sauƙi, gaskiya da tsaro.
