Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kano ya ragu da kashi 11.5 cikin 100 cikin shekaru uku, daga yara 989,234 a shekarar 2023 zuwa 875,593 a shekarar 2026.
Raguwar ta nuna cewa an samu yara 113,641 da suka daina kasancewa cikin rukunin yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ke nuni da ci gaba a kokarin shigar da yara cikin tsarin ilimi a jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dokta Ali Haruna Abubakar Makoda, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton binciken yaran da ba sa zuwa makaranta na shekarar 2026 a Ma’aikatar Ilimi ta jihar.
Makoda ya danganta raguwar da matakan da gwamnatin jihar ke dauka wajen inganta harkar ilimi da kuma kara yawan yaran da ke samun damar zuwa makaranta.
Sai dai kwamishinan ya ce duk da wannan ci gaba, har yanzu akwai babban kalubale, ganin yadda adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya kasance mai yawa, yana mai cewa akwai bukatar kara kaimi wajen magance matsalar.
Ya bayyana cewa bayanan da aka tattara daga sassa daban-daban na jihar, tare da la’akari da shekaru da jinsi, za su taimaka wajen tsara manufofi da shirye-shiryen da za su inganta harkar ilimi.
Kwamishinan ya kuma yabawa UNICEF da sauran kungiyoyin da ke aiki a fannin ilimi bisa hadin gwiwar da suke bai wa jihar wajen yaki da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
