Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Isa-Hazo, ya ce abokan hulɗar siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba su yi watsi da shi ba, duk da bambancin da ya samu tsakaninsu kan tafiyar siyasa gabanin zaɓen 2027.
Isa-Hazo, wanda ya wakilci Mazabar Basawa a Majalisar Dokokin Kaduna kuma ɗaya daga cikin abokan siyasar El-Rufai, ya ce bambancin siyasar ya samo asali ne bayan tsohon gwamnan ya shiga jam’iyyar ADC.
A cewarsa, yayin da El-Rufai ya koma ADC, wasu daga cikin abokan hulɗarsa sun ci gaba da kasancewa a wasu jam’iyyun siyasa, amma hakan ba yana nufin sun yanke hulɗa da shi ba.
Isa-Hazo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Leadership Friday, inda ya mayar da martani kan ikirarin El-Rufai cewa wasu daga cikin abokansa da abokan hulɗarsa sun yi watsi da shi yayin da yake fuskantar shari’a.
Ya musanta hakan, yana mai cewa babu wanda ya yi watsi da tsohon gwamnan.
Sai dai Isa-Hazo ya yi zargin cewa wasu mutane na amfani da halin da El-Rufai ke ciki wajen neman ƙara tasiri a siyasa.
Ya kuma ce wasu mutane na ikirarin suna tare da El-Rufai, alhali kuwa suna bin wasu tsare-tsaren siyasa daban, inda suke amfani da sunansa kawai.
Isa-Hazo ya ƙara da cewa wasu daga cikin abokan hulɗar tsohon gwamnan sun koma jam’iyyar APC, bayan wasu mutanen da a baya suke adawa da tsohon gwamnan suka fara sake kusantar sa.
A cewarsa, wasu daga cikin mutanen da ke kusa da El-Rufai suna kallon wannan ci gaba a matsayin abu mai kyau, yayin da waɗanda suke ƙaunarsa da gaske suke ganin cewa komawar ba ita ce matakin da ya dace ba.
Isa-Hazo ya ce El-Rufai na dogaro da bayanan mutanen da ke kusa da shi
Da yake magana kan matsayar siyasar El-Rufai, Isa-Hazo ya yi zargin cewa tsohon gwamnan na iya samun bayanan da ba su cika ba sakamakon tsarewar da yake fuskanta.
Ya ce kasancewar El-Rufai a tsare na takaita damar da yake da ita na samun cikakken bayani kan abubuwan da ke faruwa a wajen wurin da yake, don haka yana dogaro da bayanan da mutanen da ke kusa da shi suke ba shi.
Isa-Hazo ya kuma ce El-Rufai bai tuntubi wasu daga cikin sahihan abokan hulɗarsa domin ya bayyana musu matsayar siyasarsa ba, tun kafin tsare shi ko kuma bayan an tsare shi.
Isa-Hazo ya sake jaddada cewa bambancin da ke tsakaninsa da El-Rufai, da kuma wasu daga cikin abokan hulɗarsa, bambancin siyasa ne kawai.
