Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Ali Musa Danmaliki, ya ce tsarin sulhu da bunƙasa harkokin gwamnati na Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da cikakken haɗin kan ‘yan siyasa a ƙaramar hukumar da Kano baki daya.
Danmaliki ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar ƙaramar hukumar, inda ya ce kawo yanzu dukkan masu ruwa da tsaki a Kumbotso sun haɗa kai, kuma suna aiki da manufa ɗaya a dukkan mazabu 11 na ƙaramar hukumar.
A cewar sa a lokacin da ya karɓi mulki kuɗaɗen shiga da ƙaramar hukumar ke samu a cikin gida bai wuce Naira miliyan 1 ba, saɓanin yanzu da ya haɓaka ya zuwa kusan Naira miliyan 4 cikin shekara guda, sakamakon inganta tattara kuɗaɗen shiga da sauye-sauyen gudanarwa.
Shugaban ya ce inganta samun kuɗin shigar ya ƙarawa ƙaramar hukumar damar samar da ayyukan more rayuwa, musamman a fannonin kiwon lafiya, samar da wutar lantarki da tallafawa al’umma, tare da yaba wa Gwamna Yusuf kan ayyukan da ya gudanar a Kumbotso, ciki har da gina cibiyoyin kiwon lafiya da gada.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Danmaliki na cewa gwamnatinsa na gudanar da mulki bisa tsarin buɗe ƙofa ga kowa tare da ci gaba da tallafawa masu buƙata, haɗin da tabbatar da cewa zai ci gaba da aiki tare da manufofin Gwamna Yusuf wajen ƙara samar da kuɗaɗen shiga, kiwon lafiya, tallafin al’umma, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa haɗin kan siyasa a Kumbotso.
