Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:05 na yammacin ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026, bayan rundunar ta samu rahoton wata hatsaniya tsakanin matan biyu da suke zaune a gida ɗaya da mijinsu.
A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa Hauwa’u, wadda ita ce mata ta biyu, ta ɗauki turmi ta bugi Jamila a goshinta, lamarin da ya sa ta faɗi cikin suma, an garzaya da ita asibitin kwararru na Bauchi, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarta, an kuma ajiye gawarta a ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da binciken gawa.
’Yan sanda sun ce an kama wadda ake zargin, sannan an kwato turmin da ake zargin an yi amfani da shi wajen kai harin a matsayin hujja.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin mayar da wadda ake zargi sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a.
