Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron ƙungiyar Association of Paediatric Surgeons of Nigeria (APSON) da aka gudanar a Bauchi, inda ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen magani ga yara, waɗanda ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin rukunin al’umma mafi buƙatar kulawa.
Ya ce ya kamata ƙwararrun likitoci su yi amfani da iliminsu da ƙwarewarsu wajen taimaka wa yara da ke zaune a yankunan da ba sa samun isasshen kulawar lafiya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage mace-macen yara da kuma inganta lafiyar al’umma.
A yayin taron, ƙungiyar APSON ta gudanar da aikin tiyata kyauta ga yara a jihar Bauchi, rahotanni sun ce an gudanar da ayyukan tiyata guda 208, bayan da aka duba kimanin mutane 1,537, wasu daga cikin ayyukan tiyatar sun haɗa da waɗanda ke da matuƙar wahala.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa harkokin kiwon lafiya da ƙoƙarin inganta kayan aiki da ayyukan ƙwararrun ma’aikatan lafiya, domin tabbatar da cewa yara a birane da karkara suna samun damar yin amfani da ingantattun ayyukan kiwon lafiya na musamman.
