Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa INEC, ta wallafa kashi 44 cikin 100 na sakamakon zaben gwamnan jihar Osun a shafinta na IReV.
Wani bincike da Premier Radio ta gudanar da misalin karfe 5:27 na yamma ya nuna cewa INEC na cigaba da wallafa sakamakon zaben, kamar yadda ta yi alkawari a baya,inda a yanzu aka samu sakamakon akwati 1657 cikin 3763 da ake dasu.
A yau ne al’ummar jihar Osun suka kada kuri’unsu domin zaben sabon Gwamnan da zai jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Jam’iyyu 15 ne ke takara a zaben. Gwamna mai ci, Ademola Adeleke, na neman sake lashe zabe a karkashin jam’iyyar Accord.
Kafin zaben, ‘yan takara biyu, Adesina Adeyemi-Doro na APGA da Simon Adewale na APM, sun sanar da janyewarsu daga takarar.
Adeyemi-Doro ya goyi bayan dan takarar APC, Bola Oyebamiji, yayin da Adewale ya bayyana goyon bayansa ga Adeleke. Sai dai duk da janyewarsu, sunayen jam’iyyun APGA da APM na nan a cikin takardar zaben.
A halin yanzu, sakamakon rumfunan zabe daban-daban na ci gaba da zuwa yayin da ake tattara sakamakon zaben.
