Kungiyar Tarayyar Turai mai sa ido kan harkokin dimokuraɗiyya a Najeriya, ta ce an samu jinkirin fara kada kuri’a, matsalolin na’urar BVAS, da kuma giɓin kayan aikin gudanar da zabe a zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa.
Kungiyar ta tura masu sa ido 823 zuwa kananan hukumomi 30 na jihar domin sanya ido kan yadda zaben ke gudana.
Da yake gabatar da rahoton farko na ranar zabe a Osogbo, Babban Daraktan Cibiyar Kula da Ayyukan yaɗa labaruna kungiyar a Najeriya, Lanre Arogundade, ya ce masu sa idon sun duba yadda aka bude rumfunan zabe, samar da kayan zabe, tantance masu kada kuri’a, yawan fitowar jama’a, halartar mata da masu buƙata ta musamman, sha’anin tsaro da sauran muhimman abubuwan da suka shafi zaben.
Kungiyar ta ce daga cikin rumfunan zabe 823 da ta tura masu sa ido, jami’an zabe da ke dauke da cikakkun kayan zabe sun kasance a rumfuna 726 ne kawai.
Rahoton ya kuma nuna cewa akwai rumfunan da ba a fara kaɗa kuri’a ba har zuwa tsakar rana. Kungiyar ta bukaci hukumar zaɓe INEC ta dauki matakin gaggawa wajen tura jami’an zabe da kayan aiki zuwa irin wadannan rumfunan, ko kuma a sake tsara zaben a wuraren da ya zama dole.
Masu sa idon sun kuma nuna damuwa kan kalubalen da wasu masu kada kuri’a ke fuskanta, musamman tsofaffi, mata masu juna biyu da mutanen da ke da nakasa (PWDs) wajen samun damar shiga tsarin zaben cikin sauki.
Dangane da tsaro kuwa, kungiyar ta bukaci jami’an tsaro su kasance a zahiri a rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamako, sannan su guji yin amfani da karfin da zai sa jama’a su ji tsoro ko kuma a su yi zargin danniya.
Haka kuma, kungiyar ta yi gargadin kada a yi kokarin gurbata tsarin bayan zabe ta hanyar sanar da sakamako ba bisa ka’ida ba.
Kungiyar ta bayyana zaben gwamnan Osun a matsayin wani muhimmin gwaji ga sabon tsarin dokokin zabe, da zai iya nuna yadda babban zaben 2027 zai kasance.
