Babbar Mai Shari’a ta Kano Ta Saki Fursunoni Bakwai Saboda Rashin Lafiya
Alkaliyar babban kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai da ke fama da matsalar rashin lafiya, bayan ta duba shari’o’in mutane 82 da ake tsare da su a gidajen gyaran hali suna jiran shari’a.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya, reshen Jihar Kano, Musbahu Nassarawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, an gudanar da aikin duba shari’o’in ne a gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse, a wani mataki na hanzarta gudanar da shari’a da kuma kare haƙƙin mutanen da ake tsare da su.
Sanarwar ta ce Mai Shari’a Abdu Aboki ta duba shari’o’in mutanen da wasu daga cikinsu suka shafe shekaru a tsare ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu yadda ya kamata ba.
A yayin aikin, alkalin ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai nan take, bayan ta yi la’akari da matsalolin lafiyarsu da kuma wasu abubuwan da suka shafi ci gaba da tsare su.
Mai Shari’a Abdu Aboki ta jaddada muhimmancin tabbatar da cewa ana gudanar da shari’a cikin adalci ba tare da jinkiri ba.
Da yake jawabi, Kwamandan Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Lakpene, ya shawarci waɗanda aka saki da su ɗauki ’yancinsu a matsayin wata dama ta fara sabuwar rayuwa.
Lakpene ya bukace su da su kasance masu bin doka tare da guje wa duk wani abu da ka iya sake jefa su cikin matsala ko kai su ga cin karo da doka.
Ya kuma yaba wa Babban Kwamandan Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa samar da yanayin da ke ba da damar kula da fursunoni cikin mutunci.
A cewarsa, irin waɗannan matakan sakin fursunoni na daga cikin hanyoyin rage cunkoso a gidajen gyaran hali, tare da tabbatar da cewa mutanen da ke tsare suna samun damar yin adalci cikin lokaci.
