Masarautar Rano ta buƙaci masu riƙe da sarautun gargajiya da su mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kan al’umma, tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa ci gaban yankunansu.
Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru ne ya bayyana hakan yayin bikin naɗin sabon Hakimin Saji, Alhaji Abba Lawan Saji (Dan Kadan Rano), da sabon Hakimin Rurum, Alhaji Ado Isa Umar (Wamban Rano), da aka gudanar a garin Rano.
Sarkin ya ce sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawar takawa wajen sasanta saɓanin al’umma, tabbatar da zaman lafiya da kuma haɗa kan jama’a ba tare da nuna bambanci ba, tare ds horan sabbin hakiman da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci, tare da kusantar al’umma domin sauraron matsalolinsu da nemo hanyoyin magance su.
A nasa jawabin, sabon Hakimin Saji, Alhaji Abba Lawan Saji, ya godewa Sarkin na Rano bisa amincewar da ya yi da shi, yana mai alƙawarin gudanar da mulkinsa cikin adalci, kiyaye dokoki da al’adun Masarautar Rano, tare da yin aiki tare da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa bikin naɗin ya samu halartar manyan masu sarautun gargajiya, jami’an gwamnati, shugabannin addinai, dattawan al’umma da dimbin jama’a, inda aka gudanar da addu’o’in fatan alheri ga sabbin hakiman da kuma neman ɗorewar zaman lafiya da ci gaban Masarautar Rano.
