
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kwamitin gwamnatin jihar Kano mai yaki da gine-ginen da aka yi ba ba bisa ka’ida ba ya umarci a gaggauta cire wata katafariyar kofa da aka saka a kan hanya a unguwar Rimin Auzinawa da ke Tudun Yola C, a karamar hukumar Ungogo.
Shugaban kwamitin, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ne ya bayar da umarnin a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyarar da ya kai unguwar bayan korafe-korafen da mazauna wurin suka shigar.
Dakta Sani, wanda shi ne Darakta Janar na hukumar tsara Taswirar Filaye ta Jihar Kano (KANGIS), ya ce ziyarar ta biyo bayan wata wasikar koke da al’ummar Rimin Auzinawa suka rubuta, inda suka zargi Magaji Isyaka Mai Hula da mayar da hanyar shiga unguwar mallakarsa.
A cewarsa, masu koken sun yi zargin cewa Mai Hula ya saka katafariyar kofa a tsakiyar hanyar, lamarin da ya hana mazauna unguwar zirga-zirga cikin ‘yanci duk da yawan roko da kuma umarnin da ‘yan sanda suka ba shi kan ya cire kofar.
Dakta Sani ya umarci Mai Hula da ya cire kofar nan take, yana mai gargadin cewa gwamnati za ta dauki matakin da ya dace idan ya yi watsi da umarnin.
Haka kuma ya umurce shi da ya gurfana a gaban kwamitin tare da Takardar Mallakar Fili (Certificate of Occupancy) da kuma sahihiyar shaidar izinin gini.
Shugaban kwamitin ya yi Allah wadai da tare hanyar da al’umma ke amfani da ita, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin tsara birane da kuma koyarwar addinin Musulunci.
Ya ce, “Gwamnatin Jihar Kano ba za ta lamunci duk wani gini ba bisa ka’ida ba wanda ke hana jama’a walwala, yana jefa mazauna yanki cikin wahala ko kuma haifar da barazana ga tsaro.”
Ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen kare muradun jama’a, kuma ba za ta zuba ido tana kallon wasu mutane suna gallaza wa al’umma ta hanyar ayyukan da suka saba wa doka ba.
Da yake magana a madadin mazauna yankin, lauyan al’ummar, Barista Aminu Garba Sabonsara, ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta yi gaggawar amsa koken da suka mika mata.
Ya ce matakin da gwamnatin ta dauka ya nuna yadda manufar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta *”Kano First”* ke fifita muradun al’umma fiye da bukatun wasu masu fada a ji.
Barista Aminu Garba Sabonsara ya kuma yaba wa Kwamitin Musamman na Gano Gine-ginen da ake yi ba Bisa Ka’ida ba karkashin jagorancin Dakta Dalhatu Aliyu Sani bisa kokarinsa na tsaftace jihar Kano daga gine-ginen da suka saba wa doka tare da tabbatar da bin ka’idojin tsara birane.
Tun da farko dai mazauna unguwar Rimin Auzinawa sun roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki kan lamarin, inda suka yi zargin tare musu hanya, bayan da Magaji Isyaka Mai Hula ya saka katafariyar kofa a hanyar shiga unguwar, lamarin da ya hana al’umma amfani da hanyar.
