Majalisar Zartarwa gwamnatin Kano ta amince da kashe fiye da Naira biliyan 55 da miliyan 475 domin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a sassan ilimi, lafiya, tituna, samar da ruwan sha, gidaje, muhalli da raya karkara a faɗin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin bayani kan sakamakon zama majalisar na 40, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.
Waiya ya ce bangaren ilimi ne ya fi samun kaso mai tsoka, inda aka amince da gyara da gina makarantu da dama, samar da azuzuwa, dakunan karatu, dakunan kwamfuta, kujeru da tebura, biyan kuɗin ciyar da ɗaliban makarantun kwana, samar da kayan koyarwa ga makarantun masu buƙata ta musamman, da kuma kafa Cibiyar Koyon Zamani ta Maryam Abba Yusuf a Rijiyar Gwangwan.
A bangaren lafiya kuwa, majalisar ta amince da ginawa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a ƙananan hukumomi daban-daban, samar da kayan aikin likitanci ga asibitoci, tare da faɗaɗa wasu cibiyoyin lafiya domin ƙara inganta ayyukan jinya ga al’umma.
Haka kuma, an amince da manyan ayyukan ginawa da gyaran tituna, samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana, gyaran magudanan ruwa, da kuma aiwatar da ayyukan da za su inganta zirga-zirga da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Majalisar ta kuma amince da biyan diyya ga masu gidaje, filaye da gonakin da ayyukan gwamnati suka shafa, gina katanga da ƙofofin shiga a wasu sabbin birane, tare da sakin kuɗaɗen tallafin raya karkara domin bunƙasa rayuwar al’umma.
A bangaren yaɗa labarai kuwa, gwamnatin jihar ta amince da sayen sabbin kayan aikin yaɗa shirye-shirye ga Gidan Rediyo da Talabijin na Kano, horas da jami’an yaɗa labarai da kuma gyaran ofishin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida.
Har ila yau, majalisar ta amince da aika wasu muhimman kudurorin dokoki zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano, musamman waɗanda suka shafi inganta harkar kiwon lafiya da cibiyoyin horas da ma’aikatan lafiya.
Sannan majalisar ta ayyana rashin amincewa da dukkan wata ɗabi’a wadda take da alaƙa da harkar Daba, tare da umartar hukumomin tsaro su ɗauki matakan da suka dace domin dakile ta.
Majalisar ta kuma yaba da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana, tare da karɓar rahotanni kan ci gaban da aka samu a fannin samar da ruwa, tsara birane da kuma damar tattalin arzikin masana’antar Halal, waɗanda gwamnatin ta ce za su taimaka wajen bunƙasa ci gaban Kano.
