Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin fashin adaidaita sahu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2026.
A cewar sanarwar, Ofishin ’Yan Sanda na Dala ya samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 11:30 na daren Talata, 21 ga Yuli, 2026, bayan da wasu mutane suka yi wa Abdulrahman Atula, mai shekara 22, fashi.
Rundunar ta ce ana zargin mutanen sun yaudare shi tare da ba shi wani abu mai sa maye, kafin su ƙwace masa adaidaita sahunsa.
Sanarwar ta ce nan take jami’an ’yan sanda suka fara bincike tare da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar wasu mazauna yankin, lamarin da ya kai ga kama Usman Ashiru, mai shekara 26, da Abubakar Ali, mai shekara 28, dukkansu mazauna Rijiyar Lemo.
Rundunar ta ce an kuma ƙwato adaidaita sahun da ake zargin an sace daga hannun waɗanda ake zargin.
Kazalika, an kai Abdulrahman Atula Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin samun kulawar likitoci.
