Gidajen mai na MRS, abokan hulɗar Matatar Dangote, sun shafe aƙalla kwanaki bakwai a rufe bayan ƙaruwar farashin fetur.
Binciken da DAILY POST ta gudanar ya nuna cewa gidajen mai na MRS da ke Abuja da kewaye sun rasa wadatar man fetur tun daga ranar 17 ga Yulin 2026.
Wani manaja a ɗaya daga cikin gidajen mai ya ce suna sa ran samun mai bayan da Matatar Dangote ta koma sayar da fetur da naira ta hanyar tashar lodin ta a ranar Alhamis.
Ko a makon da ya gabata, Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur da naira a ranar 15 ga Yuli, kafin ta dawo da sayarwar a ranar Alhamis, inda ta ƙara farashin lita daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,215.
A halin yanzu, ana sayar da litar fetur tsakanin Naira 1,300 da Naira 1,340 a wasu sassan Abuja.
