Jigo a jam’iyyar APC daga Ƙaramar Hukumar Kabo, Fahad Adamu Dankabo, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga manufar “Kano First” da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa, yana mai cewa manufar ita ce ginshiƙin ci gaban Kano birni da karkara.
Dankabo ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a Shafin sa na Facebook, inda ya ce karewa da marawa manufar Kano First baya zai taimaka wajen ƙarfafa nasarorin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma bunƙasa ci gaban jihar.
Ya kuma yabawa ƙwazon kwamishinan Ƙasa na Kano Abduljabbar Garko, bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ciyar da manufofin gwamnatin gaba.
Fahad Dankabo ya kuma sha alwashin cewa al’ummar Ƙaramar Hukumar Kabo za su ci gaba da bayar da gudummawarsu domin tallafawa manufofin gwamnatin Kano da kuma ci gaban jihar baki ɗaya.
