Kwamshinan yada labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ne kaɗai ɗan takarar da yake neman mulkin jihar da gaske kuma mai mai kyakkyawar manufa, ragowar ‘yan takarar duka tarkace ne.
Waiya ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da shugabancin ƙungiyar tsofaffin kansiloli na Kano ta kudu da Kano ta arewa.
Kwamared Waiya ya ce tunda farko ya amince ya karɓi muƙamin kwamishina da Gwamna Abba ya bashi ne domin ya taimakawa ‘yunkurin gwamnan na ciyarwa da bunƙasa jihar Kano ba wai dan ya tara kudi ba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishina Waiya na yiwa tsofaffin Kansilolin alƙawarin isar da dukkan bukatun su ga gwamnatin Kano domin daukar matakin da suka dace.
