Gwamnatin Kano ta ce zata ci gaba da ƙarfafa matakan kare bayanan jama’a, yayin da gwamnati ke faɗaɗa ayyukan sauya fasalin ayyukanta, ta hanyar fasahar zamani.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taron horaswa kan tsarin tafiyar da bayanai ga gwamnatocin jihohi.
Gwamnan wanda mataimakin sa Murtala Sule ya wakilta, ya ce wajibi ne bunƙasar fasahar zamani ta tafi kafada da kafada da kare sirrin jama’a, tabbatar da ɗaukar nauyi da kuma tsaro, domin gudun kada amfani da fasaha wajen inganta ayyukan gwamnati ya tauye haƙƙoƙin al’umma.
Gwamna Abba ya ce bayanai sun zama daga cikin muhimman abubuwan dogaro wajen gudanar da mulki a zamanan ce kasancewar gwamnati ce ke kula da muhimman bayanan jama’a a fannonin da suka haɗa da ilimi, lafiya, haraji, aiki, tsaro da kuma tallafin jin ƙai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito mataimakin gwamna Garo na jaddada cewa kare bayanan jama’a nauyi ne na kowa, tare da kira ga mahalarta taron su mayar da hankali kan horar da ma’aikata, ƙarfafa tsaron bayanai, daidaita hanyoyin samun damar bayanai da kuma yadda ya dace a adana da raba bayanan bisa doka da tsari.
