Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta duƙufa domin ganin Kwalejin Fasaha ta Gaya ta zama cikakkiyar makaranta, tare da fara harkokin karatu a cikin zangon karatun da muke ciki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi rahoton ci gaban aikin kafa kwalejin daga Kwamitin aiwatar da aikin, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa mambobin kwamitin bisa jajircewa, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da dukkan tallafin da ake buƙata domin ganin an kammala aikin.
A cewar gwamna Abba, kafa Kwalejin Fasahar ta Gaya wani muhimmin yunƙuri ne na bunƙasa ilimin fasaha da koyon sana’o’i, tare da baiwa matasan Kano damar samun ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen dogaro da kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, a nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tuƙuru har sai kwalejin ta zama cikakkiyar makaranta mai aiki, tare da cika manufar da aka kafa ta.
