Gwamnatin Kano ta bukaci manya da ƙananan ’yan kasuwa da kamfanoni, da su marawa ƙoƙarin ta baya, wajen kaucewa sayar da kayan abinci da abubuwan sha waɗanda wa’adinsu ya ƙare ko suka gurɓace ga al’ummar jihar.
Shugaban hukumar kare hakkin masu saye da sayarwa ta Kano, Dr Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana haka lokacin da yake karɓar kayan abubuwan sha da wa’adinsu ya ƙare, na fiye da naira miliyan 28 wanda a kamfanin Sufaye ya miƙa mata bisa ra&in kan sa domin ɗaukar matakin da ya dace.
Dr Ibrahim ya ce matakin da kamfanin ya ɗauka yana da muhimmanci wajen kare lafiyar al’ummar Kano da kuma rage barazanar ɓarkewar cututtukan da ba’a san musabbabin su ba.
Dr Ibrahim ya ce hukumar sa za ta ci gaba da sa ido a kasuwanni, kamfanoni da wuraren sayar da abinci domin tabbatar da ganin kayan da ake sayarwa ga al’umma sun cika ƙa’idojin lafiya da inganci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Ibrahim na fatan matakin da kamfanin na Sufaye ya ɗauka zai buɗe ƙofa ga sauran manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni masu kishin ci gaban Kano su dinga miƙa kayan da suka lalace ko wa’adinsu ya ƙare ga hukumar, maimakon mayar da su kasuwa.
