Rahotanni sun ce harin na da alaƙa da wani jagoran ’yan bindiga da ake kira Malan Shuaibu, wanda ake zargin ya kai harin ne domin ramuwar gayya bayan hare-haren da jami’an tsaro suka kai wa ƙungiyarsa.
Wata majiyar tsaro ta ce sojoji sun shiga yankin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindigar sun tare hanyoyi inda suka fara sace matafiya.
Mazauna yankin sun ce a kwanakin baya jami’an tsaro sun kama wasu mutanen da ake zargin suna bai wa ’yan bindigar bayanai da kayayyaki, ciki har da wasu da ake zargin suna yi musu hada-hadar kuɗi ta POS.
Majiyar ta ce ana zargin Shuaibu da yaransa sun fusata ne bayan kama mutanen da ke taimaka musu.
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 8, Operation “Fansan Yamma”, Laftanal Kanal Olaniyi Soba, da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Laftanal Kanal Aliyu Danja, sun tabbatar da faruwar lamarin.
