Hukumar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da shirin Auren Gata daga ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026.
Hukumar ta kuma yi kira ga duk waɗanda aka tantance domin cin gajiyar shirin da su ziyarci sakatariyar ƙananan hukumominsu domin karɓar duk wani tallafi da Gwamnatin Jihar Kano ta tanadar musu.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce ba za a bai wa kowa wani tallafi ba sai ya gabatar da katin shaidar tantancewa, domin tabbatar da cewa yana cikin waɗanda aka amince da su a shirin.
Dakta Mujahiddeen ya ƙara da cewa kowace ƙaramar hukuma za ta jagoranci ma’auratan da ke ƙarƙashinta zuwa masarautar da suke ƙarƙashinta domin gudanar da daurin aure.
